TARIHIN ALHAJI BARAU BAKORI

Ga ƙarin bayani kan tarihin Alh. Barau.

Wasu sun ɗauka cewa shi kaɗai ne mahaifiyarshi ta haifa, to ba haka ba ne. 

Ya na da yaiye guda 3 waɗanda su ke uwa ɗaya amma ba uba ɗaya ba; mace ɗaya, maza 2. Macen ita ce babba, sunanta Hauwa kuma ana ce ma ta Tagudu ko Yaya, kuma ita ce Gwaggo wadda dalilin ta ne aka laƙaba ma Baba Ɗangwaggo wannan sunan. Ita ce uwar Alh. Tafida, baban su Yaro-Ƙasimu. Sannan, ita ta haifi Baba Inuwa da Baba Ɗantsoho, baban su Tani da Azumi. 

Mai bi ma ta sunan shi Musa, ana ce ma shi Dodo. Sunan shi ne a ka sa ma Baba Mairiga. 

Na ukkun sunanshi Abdullahi, wanda a ke ce ma Sambo. Shi ne a ke ma Alh. Barau kirari da shi, ana cewa, "Barau na SAMBO, jikan Galadima...". Shi Sambon kuma shi ne baban su Alh. Hassan na Kano da Gwaggo Yalwa, Yarinya da Sharubutu, uwar su Nata'Ala da Hassatu, uwar su Ɗalibi.

Daga nan sai mahaifiyar Alh. Barau ta auri baban shi, a ka haife shi. Shi kaɗai ta haifa a gidansu. Kuma ta zo gidan su Alh. Barau da ƴaƴanta maza 2 daga wancan gidan. Ita macen, watau Gwaggo ɗin, lokacin ta riga ta yi aure. Shi kuma Alh. Barau a gidansu, ya na da ƴar'uwa mace, yayarshi, ubansu ɗaya amma ba uwarsu ɗaya ba, ita ce Hajiya Nanne ta Kano. Sai a ka haɗa aure tsakani yayar Alh. Barau, Hajiya Nanne wadda su ke uba ɗaya da kuma wan shi, Abdullahi (Sambo), wanda su ke uwa ɗaya. Shi ne su ka haifi su Alh. Hassan, Gwaggo Yarinya, Yalwa, Hassatu da Sharubutu, mahaifiyar su Nata'ala. 

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post