TARIHIN IBRAHIM NAMOWA BAKORI

Shi Ibrahim Namowa Bakori, kakana wanda ya haifi uwata, bafillace ne na ƙasar Daura, waɗanda a ke ce ma Dauraji. An haife shi a Daura inda ya ke yi ma iyayenshi kiwon shanu.

Daga Daura sai su ka tashi su ka koma Ingawa su ka yada zango. Daga nan su ka koma Dayi, sai Gozaki, sai wani ƙauye kusa da Shika, Bijimi. Daga Bijimi ne su ka dawo Tandama.

A Tandama ne da ya girma ya koma harkar kasuwanci, ya na  sai ma Turawa gurya a matsayin agent. Nan ne su ka shaƙu da wani ɗankasuwan mai cinikin goro, ana ce ma shi Malam Barau. Sun shaƙu, su ka zama aminai, har wani lokaci kafin Turawa su kawo ma Namowa kuɗin ciniki in na hannun shi ya ƙare, ya kan amshi rance wajen Malam Barau, in Turawa su ka kawo sai ya mayar ma M. Barau kuɗinshi.

Suna nan a haka sai Turawa su ka ce Namowa ya koma Bakori ya riƙa sai ma su Auduga don an buɗe huloti. Sai Namowa ya shawarci M. Barau cewa su koma Bakori. Ya kuma ce ma shi shima ya shiga harkar sayen Auduga ɗin. Haka kuma a ka yi. Dalilin dawowar su Bakori kenan.

Saboda amintakar da ke tsakanin Barau da Namowa, har Namowa ya aura ma Barau ƙanwarshi wadda su ke ƴaƴa maza, watau Hannatu. Kuma, su ka haɗa ƴaƴansu, Abdulƙadir da Halima (Ƴargambo ko Iya) aure. Daga baya kuma su ka ƙara haɗa wasu ƴaƴan na su aure, Muhammadu Ɗangwaggo da Turai. 

Dalilin da ya sa a ke ce ma Iya (mahaifiyata), Ƴargambo kuwa, don shi Gambon(Gambo Daura) ɗan'uwan Namowa ne, ƴaƴa maza su ke. Shine kakan Ƴar Mu'azu, shi ya haifi babanta, Ɗantine.

Namowa ya na da ƴan'uwa biyar waɗanda su ka fito gida ɗaya. Guda ukku (maza biyu, mace ɗaya) ɗakinsu ɗaya.  Guda biyu kuma, (mace ɗaya, namiji ɗaya), uba su ka haɗa.

Akwai ƙanin Namowa, uwa ɗaya uba ɗaya, ana ce ma shi Jibir Gwanin Doki. Kuma ana ce ma shi Baban Ƴargambo (Iya). Kuma ya na da wani ƙanin uwa ɗaya uba ɗaya sunanshi Garba (Abubakar), sunan da a ka sa ma kawu Sambo kenan. Amma da shi Jibir ɗin da Garba ba wanda ya taɓa haihuwa. Bayan su kuma, yana da ƙanwa, ita ma uwa ɗaya uba ɗaya ana ce ma ta Gwaggon Zaria, ita ta haifi Abun Kanti ta Zaria da Inna Ƴambiyu ta Kaduna.

Sannan ya na da ƙanwa, Mairo, wadda su ke uba ɗaya. Ita ta haifi uwar Hajiya Azumi ta Minna, Hauwa, da Ladan, da Tanko (Salihu), baban Ariguna (Habiba). Kenan, Ariguna tsatson Namowa ce ta wajen uwa da uba: uwarta, Deluwa, ɗiyar Namowa ce, babanta kuma jikan ƙanwar Namowa ne wadda su ke uba ɗaya. 

A Tandama kuma akwai sauran ƴan'uwan Namowa waɗanda su ke ƴaƴa maza, su shida. Akwai Muƙaddas-Yero, a Tandama ya ke, kuma shi ya haifi Lawal, wani nurse wanda ke Funtua da kuma Ali, wanda ke CBN, Abuja. Akwai kuma Ɗanmusa, baban Suleiman, wanda ke aiki Hassan Usman Katsina Polytechnic. Sannan akwai Dije, uwar Kawu Mudi, baban Safare ta Minna. Akwai kuma Hannatu, uwar su Alhaji Shehu, Ƴardada, Alh. Ɗangwaggo, Alh. Amadu da Alh. Mairiga. Sauran ƴan'uwan Namowa su ne Gambo Daura da Baba Lawal.

Ibrahim Namowa ne mutum na farko da ya fara sayen mota a garin Bakori. 

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post