Daga Gwagware Media Reporters
Ƴan takarar gwamna na jihar Katsina da za su fafata a zaɓen 2023 sun sanya hannu kan shirin zaman lafiya na 2023 wanda hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kan ta, wato (INEC) reshen jihar Katsina ta shirya, a babban ɗakin taro na ƴansanda da ke titin Kangiwa, GRA, Katsina, ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu 2023.
Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina karkashin tutar jam'iyyar APC, Dakta Dikko Umaru Radda, ya na ɗaya daga cikin ƴan takarar da su ka samu halartar taron.
A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ya shaida ma su cewa, wannan yarjejeniya za ta karfafa damokaraɗiyya a jihar Katsina. Sannan, ya tabbatar da bada cikakken haɗin kai don ganin an yi zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana. Kuma, ya bayyana cewa zai karɓi sakamakon zaɓe ko wane iri muddin an yi shi a cikin inganci da sahihanci.
Shugaban hukumar fararen kaya, wato, DSS, ya gode ma ƴan takarar gwamna, shugabannin jam'iyyu, iyayen ƙasa da kuma jami'an tsaro yadda su ka nuna haɗin kai da goyon baya don ganin an gudanar da zaɓe cikin zaman lafiya.
Tags
Hausa News