An Yi Kira Ga Jami'an Kiwon Lafiya Da Su Zaɓi Dikko Raɗɗa A Matsayin Gwamnan Katsina

Daga Katsina Post 

Hajiya Zainab Tafashiya 

Hajiya Zainab Tafashiya tsohuwar  shugaban bangaran  horar da malaman asibitin karkara, ta makarantar koyan kiwan lafiya ta Kankia (HOD) ta nemi alfarmar ɗaliban da malaman makarantun kiwon lafiya da su zaɓi Dr. Dikko Raɗɗa. 

Hajiya Zainab Tafashiya Ta  ziyarci  makarantun horar da aikin kiwan lafiya, na jahar Katsina da masu zaman kansu inda ta roki alfarmar abokan aikin ta, da kuma faɗakar da ɗalibai  akan mahimmancin zaben jam'iyar APC SAK daga kasa har sama.


Hajiya Zainab Tafashiya tayi kira ga ɗaliban kiwan lafiya dasu riƙe karatun su da kyau, su dage ga aikin su don karatu ne mai albarka.

Sannan tayi kira ga ɗaliban dasu zabi chanchanta da shuwagabanni masu ilimi da tsoron Allah.

Ayayin ziyarar ta makarantar kiwon lafiya A Kankia ta jaddada zaɓen, Tinubu, Dikko, da Nasiru sani zangon daura a matsayin sanator daura zone, Abubakar Yahaya Kusada a matsayin ɗan majalisar tarayya Kankia, Kusada, Ingawa, da salisu  Rimaye mai gemu a matsayin ɗan majalisar jiha. 

Haka ma a Daura ta ziyarci makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu ta ƙarfafa zaben APC Sak.

Katsina Post ta samu cewa ɗaliban a SHT Daura sun shirya Drama mai dauke da bayanin ƙudurin gidan Dikko ɗantakarar APC da Abokin takar shi.

Hajiya Zainab Tafashiya ta ba daliban tallafin kayan rubutu da karatu, Riguna da kuma huluna. 

Malamai da dama sun tofa Albarkacin bakin su a makarantar koyon aikin kiwon lafiya a Daura da Kankia Da makarantu masu zaman kansu.

Abokan Aikin Hajiya Zainab na AFCOHWA sunyi kira ga daliɓani a makarantu masu zaman kansu cikin Katsina da su mai da hankali ga karatu kuma su zabi jam iya mai tsintiya 

A Daura Hajiya Zulaihat co-ordinator Dikko Jobe consultative Forum, ta wakilci uwar wannan ƙungiya Hajiya Hauwa Umar Raɗɗa tayi kira ga yan daura suyi  APC SAK.

Shugaban matasa na tafashiya Nura Ra 'I  ya kara wayar ma da mata kai kan Amfanin zaben 
APC.

Daga nan ya gode ma Hajiya hauwa umar Raɗɗa shugabar Dikko jobe consultative forum, Nasif  Ahamad Bakori, ƴankungiyar AFCOHWA da sauran waɗanda suka halarta.

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post