Labari Da ɗumi-ɗumi!
Jam'iyyar APC a jihar Katsina, ta lashe zaben kujerun sanatoci guda uku da ƴan majalisar wakilai ta taraiya guda tara, yayin da jam'iyyar adawa ta PDP a jihar ta sami kujerun majalisar wakilai ta taraiya guda shidda.
Sanatocin sune:
(1) Sanata Abdul'Aziz Musa Ƴar'Adua mai wakiltar Katsina ta tsakiya.
(2) Sanata Nasiru Sani Zangon Daura mai wakiltar shiyyar Daura.
(3) Sanata Muntari Ɗandutse mai wakiltar shiyyar Funtua.
Ƴan majalisar taraiya guda tara da Jam'iyyar APC ta lashe zabensu sune:
(1) Kaita da Jibia Hon. Sada Soli Jibia.
(2) Kurfi da Dutsinma Hon. Aminu Balele Dan-Arewa.
(3) Batagarawa, Rimi da Charanci Hon. Usman Banye.
(4) Daura, Sandamu da Mai'adua Hon. Aminu Jamo Daura.
(5) Mani da Bindawa Hon. Ahmed Yusuf Ibrahim Doro (Ayid).
(6) Baure da Zango Hon. Sani Lawal Baure.
(7) Musawa da Matazu Hon. Abdullahi Aliyu Janaral.
(8) Kafur da Malumfashi Hon. Aminu Ibrahim Kafur.
(9) Funtua da Dandume Hon. Barr. Abubakar Gardi.
Ƴan majalisar wakilai ta taraiya guda shidda da Jam'iyyar adawa ta PDP ta lashe zaɓensu sune:
(1) Mashi da Dutsi Hon. Salisu Yusuf Majigiri
(2) Kankia, Kusada da Ingawa Hon. Samai'ila Dalha Kusada.
(3) Bakori da Danja Hon. Abdullahi Balarabe Dabai.
(4) Kankara, Sabuwa da Faskari Hon. Jamilu Lion.
(5) Safana, Batsari da Danmusa Hon. Ali Ilyasu Dan-Alhaji.
(6) Karamar hukumar Katsina Hon. Aminu Chindo.
Amma kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya doke abokin hamaiyarshi na jam'iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu, a jihar Katsinan da ƙuri'u 489,045 a yayin da Tinubu ya sami ƙuri'u 482,283 wanda ya nuna banbancin ƙuri'u 6,752.
27 February, 2023.
Tags
Hausa News