Tinubu Ko Atiku? Ina Mafita Ga Arewa?

Daga Maiwada Dammallam


Nazari Da Hangen Nesa:

Duk wata matsaya da za mu dauka a zaɓen da ke tafe nan da ƴan kwanaki kaɗan, ya na da kyau mu sa nazari da hangen nesa da kuma ɗauko tsohon tarihi na baya da duba gabanmu. Allah SWT ya halicce mu da hankali domin mu rika iyo a cikinsa, kuma wannnan hankalin shi ne a ka ce bambancin mutum da dabba. Surori da ayoyi masu yawa a cikin Alkur’ani mai tsarki bayan kawo misali na tarihi, sai Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: "Ko ba ku lura ba ne?" Wasu ayoyin a cikin Alkur’ani mai tsarki, za ka ji suna hannunka mai sanda domin yin nazari a kan muhimmancin yin tunani da kuma hangen nesa.

Wannan zaɓen da za a yi na Shugaban Kasa a ranar 25 ga Fabrairu, tsakanin Alhaji Bola Ahmed Tinubu da Alhaji Atiku Abubakar, wani zakaran gwajin dafi ne na neman mafita ko kuma shiga tsaka mai wuya ga al’ummar Arewa da makomarta. A kan haka na bi tarihi don in ƙara faɗaɗa mahawarar da ke gudana game da ingancin manyan yan takarar da a ke ma kallon su ne kan gaba a zaɓen. Amfanin tarihi dama shi ne mutum ya gane daga ina ya fito, kuma ina ya nufa. 

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyar APC, Bayarabe ne haifaffen jihar Legas daga kudancin Nigeria. A tarihi, jihar Legas, kamar sauran jihohin yankin Yarbawa, ta na da tsohon tarihi na kyakkyawar zamantakewa da mutanen Arewa tun kafin zuwan Turawa. Musulunci ya zo wa Arewa ta Sahara, yayin da ya je wa Yarbawa ta ruwan teku. Addinin Musulunci shi ne wanda ya fara haɗa kan Musulmin Arewa da kuma na yankin Yarbawa. Kusan haka tarihin ya ke ga abokan zamanmu na addinin Kirista. Kirastanci ya zo ta ruwa, wasu kuma ta Sahara, duk an haɗe a Arewa domin yada addinin. Bayan haɗuwar yaɗuwar addini, kasuwanci ya haɗa mutanen Arewa da Kudu sama da shekaru 100 kafin zuwan Turawa.

Masana tarihi za su tabbatar cewa rubuce-rubucen da Turawan mulkin-mallaka su ka yi, sun tabbatar lokacin da su ka zo Legas sun samu cewa kabilun da Yarbawa suka fi mu’amala da su sune mutanen da su ka fito daga Arewa ba tare da la’akari da addinin da kowacce ƙabila ta fito daga Arewa ba. A kiyasi, masaukai na mazauna ƴan Arewa a bangarorin kasar nan, sun fi yawa a jihohin Yarbawa. Kusan kowanne yanki a jihohin Yarbawa, akwai “Zango” na ƴan Arewa waɗanda sun kai shekaru daga 80 zuwa sama; ninkin baninkin fiye da na wasu yankunan kasar nan.

A siyasa, tun kafin ƴancin kai, Yarbawa na haɗa kai da ƴan Arewa ne a wajen cimma muradu na siyasarsu. A zamanin mulkin Tafawa Balewa, Yarbawa da ’yan Arewa sun rika magana da murya ɗaya ne. A yaƙin basasa, Yarbawa sun mika wuya ga kasantuwar Nijeriya ta zama ƙasa ɗaya. A fagen daga an rika yaƙi kafaɗa da kafaɗa da Yarbawa, wasu ƙananan kabilun kudu da kuma ƴan Arewa, wanda ta kai har a ka yi nasarar tabbatuwar Nijeriya a matsayin ƙasa ɗaya.

Bola Ahmed Tinubu ya zama wani misali na yadda tun da a ka fara wannan dimokaraɗiyya a shekarar 1999 ya ke tafiya tare da Arewa cikin yarda da amana. A zaɓen shekarar 1999 ya goyi bayan Arewa ne ya juya wa Olusegun Obasanjo baya. Da Obasanjo na neman tazarce, Bola Tinubu ya goyi bayan ƴan Arewa a yaki da wannan tazarcen. Da PDP ta tsayar da Marigayi Malam Umaru Musa Ƴar’adua a matsayin ɗantakarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya mara mashi baya. Da a ka zo zaɓen 2011, Bola Tinubu ya mara ma Malam Nuhu Ribadu baya daga Arewa. A 2015, Tinubu ne ya haɗa rundunar da ta koma APC, Buhari ɗan Arewa, ya lashe zaɓe. Shi ne ƙashin bayan haɗa duk mutanen da su ka yi aikin rusa wasu jam’iyyun zuwa APC. A lokacin APC almajira ce, shi ne ƙashin bayan nemowa da samo kuɗin da a ka yi aiki har zuwa zaɓe. Kai, shi kanshi Atiku Abubakar akwai lokacin da ya garzaya wajen Tinubu domin neman mafakar siyasa lokacin da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya taso shi gaba. Kai, ƙarewa, na san da yawa ba za su manta dangantakar siyasar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Marigayi Janar Shehu Musa Yar’adua ba. 

Hakika, zaɓen Tinubu biyan bashi ne da Arewa za ta yi wanda hakan zai ƙara danƙon zumuntar da ke tsakanin Yarbawa da Arewa wadda a ka gina sama da shekaru 100. Hakan kuma zai kare kasuwanci da hulɗar da ke tsakanin Yarbawa da Arewa na sama da shekaru 100, sannan ya kare mutuncin Arewa da kuma tabbatar da yankin a matsayin mai amana wanda za a iya dogara da shi a ƙulla amanar siyasa. Zaɓen Tinubu zai tabbatar da cewa mu ƴan Arewa mutane ne masu alƙawari, waɗanda ba sa manta alheri. 

A ka kuma yi sa’a Tinubu mutum ne mai kyakkyawan tarihi a tarihin siyasar Najeriya duba da yadda mulkin shi a matsayin Gwamnan Legas ya zama wata kwaranga da ta sa jihar Legas ta fita tsara ta kuma zama abin koyi. Tsarin da ya ɗora jihar Legas ba na ɓangaranci ko kyamar juna bane. Tsari ne da ke dogaro bisa himma da basirar al’umma daga ko ina su ka fito. Ginuwa kan wannan tsarin ya sa yau akwai Bafillace, ɗan Jihar Katsina wanda ya ke riƙe da muƙamin Kwamishina a Jihar Legas. Haka da dama ƴaƴan wasu jihohi sun taka rawa a jihar Legas a matsayin waɗanda a ka dama da su a mulkin jihar Legas a matakai daban-daban, a lokuta daban-daban. Da yawa nan ƴaƴan wasu jihohi su ka sami yin fice har su ka zama wani abu a siyasar Najeriya. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Osinbajo ya na cikin wannan rukunin na waɗanda su ka amfana da irin siyasar wayewa ta Tinubu. 

Ko a yau kewaye da Tinubu da yawa mutanen Arewa ne su ka yi fice kuma a ka san su da kishin ƙasa, waɗanda su ka daɗe tsaye kan ƙoƙarin ganin Najeriya ta ɗauki saiti irin wanda ya dace da ita. Cikin su akwai irin su Malam Nuhu Ribadu wanda sananne ne wajen jagorancin yaƙi da cin hanci da rashawa ba a Najeriya ba kawai, duk faɗin duniya. A na iya cewa ma yau duk inda ɗan Najeriya ya ji an kira sunan EFCC fuskar Malam Nuhu za ta fara faɗo ma shi a rai kafin ita hukumar kanta. A ɗaya hannun manyan ƴan siyasa ne irin su Gwamna Masari, Gwamna Badaru, Gwamna Ganduje, Gwamna El-Rufai da sauran Gwamnonin Arewa masu faɗi a ji. A hamshaƙan ƴan siyasa kuwa su Malam Ibrahim Masari da Sanata Abu Ibrahim duk su ne makusantan shi na ƙut da ƙut. To wane abu Arewa za ta nema ta rasa a gidan siyasar Tinubu? 

Atiku Abubakar ɗan Arewa ne, kuma ya daɗe ya na siyasa tare da neman shugabancin ƙasar nan. Ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa na tsawon shekaru takwas. A ƙarshe, shugaban ƙasar da su ka yi aiki da shi, Olushegun Obasanjo, ya yi rubutu a kan shi, ya kuma misalta shi a mara amana da ba zaka iya dora nauyin jagorancin sama da mutane milyan dari biyu a kan shi ba. Atiku kuma ya tabbatar da haka idan har faifan da wani tsohon mataimakin shi na musamman, Mr. Michael Achimugu, ya fitar kwanaki kaɗan da su ka wuce ya isa misali. A cikin faifan, an ji sautin muryar Atiku ya na bada bayanin yadda ya sa a ka ƙirƙiri kamfanoni na bogi don fidda kuɗaɗe daga lalitar gwamnati ta hanyar zamba. Idan hakan ya tabbata, to zai zamana rashin ƙyamar cin amanar ƙasa da mutane da yawa su ke kallo, su ke jin tsoron bashi amanar Najeriya. 

A tafiyar siyasar shi kuma, kowa ya san yadda Atiku Abubakar ya yi ta canza jam’iyu daga wannan zuwa waccan don kawai zafin neman shugabanci. Duk da wannan yawo da ya yi na neman mulki, zuwa yanzu bai fito ya faɗi ma ƴan Najeriya wani sabon abu da zai yi daban da wanda ya yi lokacin da su ka jagoranci Najeriya shi da Obasanjo ba. Ƙila mai karatu ya yi tunanin mataimakin shugaban ƙasa ba shi da ikon kawo chanji. Wannan ba gaskiya ba ne. Atiku ya samu cikakkar dama wadda zai iya inganta Arewa amma sai ya yi amfani da damar wajen daƙile ci gaban Arewa. Idan kuma har ya samu damarmaki da ya inganta rayuwar shi ta shi kaɗai ta hanyar yin abubuwa kamar samar da jami’a ta shi ta kan shi, ya a ka yi bai samu damar inganta jami’o’in gwamnati da ƴaƴan talakawa su ka dogara a kai don samun ilmi ba? 

Idan har Atiku bai da ƙumbar susa a gwamnatin su da Obasanjo, yaya a ka yi a shekara ta 2004 ya samu lasisin gina jami’a ta kan shi, ta ƴaƴan masu hali daidai lokacin da jami’o’in da ƴaƴan talakawa ke dogara a kai, waɗanda su ka rantse shi da Obasanjo, za su kare martaba tare da inganta su ke tabarbarewa har malaman jami’o’i na yajin aiki don su jawo hankalin su suyi abinda ya ke daidai? To idan ya kasa a wancan lokacin, da me za mu dogara mu yi tunanin zai iya yin wani abu yanzu?

Sannan har zuwa ƙarshen mulkin su shi da Obasanjo bai taɓa buɗa baki ya yi tofin Allah tsine kan irin cin kashin da Obasanjo ya yi ma Arewa ba duk da cewa akwai manyan yan Arewa da su ka tunkari Obasanjo gaba gaɗi, su ka furzas da baƙin cikin su kan irin yadda Obasanjo ya danne hakkokin Arewa, ya kuma riƙa fifita Kudu. Na san dai mai karatu ba zai manta yadda Sarkin Gwandu na 19, Mai Martaba Al-Mustapha Haruna Jokolo, ya tirke Obasanjo kan wannan dalilin ba, dalilin da ya sa Obasanjo ya yi ƙulla-ƙullar da a ka tsige Mai Martaba Jokolo daga kan karagar mulki ba bisa ka’ida ba. 

Duk ina Atiku a lokacin? Kuma wace rawa ya taka don hana afkuwar hakan a lokacin da a yau a ke tallar shi a matsayin mafita ga ƴan Arewa? Idan kuma wannan bai isa hujja ta rashin cancantar Atiku ba, kasancewar kusan da hannun shi gwamnatin Obasanjo ta yi ma ƴaƴanta da ƙawayenta gwanjon duk wani kamfani na gwamnati da ke da tasiri a tattalin arzikin Najeriya ta isa ta ankarar da mutane cewa Atiku da ci gaban Arewa hannun riga su ke. Sanin kowa ne dai ko Najeriya bai zama bayan kakar zaɓe. Da ya faɗi zaɓe sai ya tattara kayanshi ya koma Dubai sai an sake busa kugen zaɓe ya dawo neman shugabanci. Kenan, a jita-jita ya ke tsintar abinda ke faruwa a Najeriya kuma a haka yake tunanin zai gyara Najeriya. Ko hakan na yiwuwa ko bai yiwuwa, dabara dai ta rage ma mai shiga rijiya. 

Abin kula dai shi ne, tarihin siyasar Atiku ya nuna cewa son ransa da bukatar kanshi ya sa farko a gwargwarmar neman mulkin da ya daɗe ya na yi. Duk wata mahanga ta hankali ta nuna cewa zaɓen sa matsayin shugaba hatsari ne ga ƙasa da kuma Al'ummar Arewa.

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post