Daga Gwagware Media Reporters
A ranar Talata, 21 ga watan Maris 2023, shahararren ɗan kasuwar nan, Alhaji Ɗahiru Bara'u Mangal, ya ziyarci zaɓaɓɓen gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda, domin taya shi murnar lashe zaɓen da ya yi na ranar Asabar, 18 ga watan Maris, 2023.
Alhaji Ɗahiru Mangal, ya yi addu'ar samun nasarar tafiyar da gwamnati tare da yi ma Dr. Radda fatan alkhairi.
Da ya ke jawabi, Dr. Dikko Radda, ya yi godiya bisa ga wannan ziyara da aka kawo mashi tare da bada tabbacin kawo kyakkyawan shugabanci don ganin jihar Katsina ta kai mataki na gaba.
Tags
Hausa News