Daga Katsina Post
Gwamna Aminu Bello Masari ya ƙaddamar da kwamitocin miƙa mulki ga sabuwar Gwamnatin jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin zaɓaɓɓen Gwamnan jihar, Dr. Dikko Raɗɗa.
A ranar 18 ga watan Maris a ka gudanar da zaɓen Gwamna a jihar Katsina wanda Dr. Dikko Raɗɗa ya lashe zaɓen ƙarƙashin jam'iyyar APC, za'a kuma miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun bana.
Sakakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal, shi ne zai jagoranci kwamitin miƙa mulkin mai membobi 40 sai kuma Kwamishinan Ruwa da albarkatu, Musa Adamu Funtua, shi ne zai jagoranci kwamitin shirye-shirye da tsare-tsare, wanda ke ɗauke da membobi 43.
Da ya ke jawabi yayin ƙaddamarwar, Masari ya yi kira ga Kwamitocin da su yi aikin tuƙuru don ganin an cimma nasarar miƙa mulki kamar yanda a ka tsara.
Sannan ya roƙi Allah da ya ba kwamitocin damar aiwatar da aikin su don al'ummar jihar Katsina su cigaba da cin gajiyar mulkin jam'iyyar APC da ke tabbatar da romon damokaraɗiyya.
Tags
Hausa News