Dr. Radda: Ko Da Naka Ka So Nagari


Daga: Adamu S. Ladan 

Asabar ta karshen satin nan ne mutanen Najeriya za su sake fita don zaben wasu shugabanni amma a  matakin jihohi. 

Za a zabi gwamnoni da 'yan majalisun jihohi. 

Za a gudanar da zaben ne a jihohi talatin da daya, (31) daga cikin 36 da ke kasar nan. Jihohin da ba za a gudanar da zaben ba su ne, Kogi da Imo da Bayelsa. 

Daga zaben da aka gudanar a kwana nan ta bayyana a fili takarar gwamnan jihar Katsina, gwagwarmaya ce tsakanin jam'iyyar APC da ta PDP. 

Idan ba a manta ba zaben da aka yi a shekarar 2019 maigirma gwamna Aminu Bello Masari ya lashe zaben ne da fiye da kashi 70 cikin 100 na kuri'un da aka kada, watau (70.4%). 

Wannan karon jam'iyyar APC na gabatar da Dr. Dikko Umar Radda a matsayin dan takar ta, yayin da PDP ke gabatar da sanata Yakubu Lado Danmarke. 

Dantakarar jam'iyyar APC, Dr. Radda shine tsohon shugaban cibiyar ciyarda da kanana da matsakaitan masana'antu gaba ta Najeriya, watau (SMEDAN). 

Dan shekaru 54,  Dr. Radda gogaggen dan siyasa ne, kwarere kan harkar zuba jari, tsohon malamin makaranta, da aikin banki kuma goggen masanin tafiyar da mulki. Ya fito ne daga shiyyar mazabar Katsina ta tsakiya. 

A daya hannu kuwa baya ga  cewa dan kasuwa ne, ba a san wani abu na tarihi game da sanata Yakubu Lado wanda rahotonni su ka nuna cewa ya shiga siyasa tun kafin karanshi ya kai tsaiko. Bai da wani tarihi na aikin gwamnati ko tafiyar da jama'a in banda zaman sa a majalisun wakilai da na dattawa lokacin da mulkin jam'iyyar PDP ke damawa a sha yadda ta so. 

Duk da cewa akwai sabani game da shekarun sa, sanata Lado dan shekaru 62, a wani kaulin fa fito ne daga yankin mazabar kadancin jihar Katsina. Yankin da gwamna mai ci ya fito.

Hakika jiha kamar Katsina na bukatar jagora lafiyayye, tsayayye, mai dogaro da kansa, mai ilmi kuma kwararai akala a wa su fannoni na rayuwar aikin gwamnati ko kampanoni ma su zaman kan su. 

Jihar Katsina ba ta bukatar jagora yankan rake, ko dan bani na iya wanda ba zai iya rabe baki da fari ba. 

Ga Dukkan alamu zaben ranar Asabar mai zuwa dauraya ce ga jam'iyyar APC. Ba dan komai ba sai la'akari da dalilai ma su dimbin yawa. 

Da farko dai jam'iyyar APC na da nagarta da kima a wajen jama'a jihar Katsina. Haka kuma jam'iyyar ta zabo nagartattun 'yan takara a matakin gwamna da mataimakin sa da kuma 'yan majalisun jiha. 

Idan  mu ka kalli jam'iyyar za mu iya cewa duk da yawan 'yan takaran da su ka nemi zawarcin jihar lokacin zaben fidda da gwani kimanin su goma wannan bai sa ta shiga rikicin da abokiyar hamayya ta ta PDP ke ciki. 

In banda mutum daya daga cikin 'yan takarar da ya ki rugumar kaddara da karbar sulhu da manyan ciki da wajen jihar su ka yi kokarin yi, duk sauran su na cikin jam'iyyar APC kuma da su ake damawa. 

Duk da cewa ba za a rasa 'yan korafe korafe nan da can ba, kyakkyawan shugabancin da Maigirma Gwamna Masari ya nuna na kin katsalandan a harkar gudanar da jam'iyyar da kuma lokacin zaben fidda gwani ya taimaka kwarai wajen tabbatar da adalci da zaman lafiya a jam'iyyar. 

A daya bangaren kuwa za a iya cewa a halin yanzu ba wanda ya san shugaban PDP na sahihi. Tun da ta gudanar da zaben fidda gwani jam'iyyar ta daddare zuwa gida gida. 

Matsalar kuma ta ta'azar lokacin da tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina ya koma jam'iyyar. 

Wannan rabe rabe ya raunata jam'iyyar gaya inda duk lokacin da ta yi taro za ka iske an rabu dutse hannun riga tsakanin bangarorin ma su mayya da juna. 

Baya ga fitowa daga babban gida, Dr. Radda ya sa mu kyakkyawar sheda cewa mutum ne mai tarbiya da halaye nagari da iya mu'amala da hangen nesa. 

Ya na kuma da tausayin na kasa da marasa galihu. Ya kan nuna matukar damuwarsa kan al'amarin al'umma. 

Duk da wadannan halaye, Dr. Radda ba mutum da aka yi wa hawan kawara ba ne musamman kan abun da ya shafi gudanar da mulki da jama'a. Ya iya tawaye akan duk wata manufa da ya ke ganin ba za ta haifar ma jama'a da mai ido ba. 

Wadanda su ka yi aiki da shi kud-da-kud sun ba da shaida cewa ya na da tsinkaye da hangen nesa wajen daukar shawara da yanke hukumci. Ya na da kuma gogewa da tsantseni wajen tusarrafi da dukiya al'umma. 

Shin ko jama'a jihar Katsina za su amfana da wadannan nagargartun halaye na Dr. Radda? 

Eh! Dr. Radda bai bar mu cikin shaku ba kan cewa zai iya jagorancin jiha kamar ta Katsina mai yawan jama'a da kwararu a kowane fanni na rayuwa.

Daga lokacin da aka tsaida shi a matsayin dan takarar jam'iyyar APC zuwa yanzu, Dr. Radda da kalaman sa da ayyukan sa sun nuna cewa jagora ne nagari. 

Daga tanade tanaden da ya yi cikin kundin da ya gabatar wa jama'a zuwa rangadin da ya gudanar da kalaman sa ya nuna cewa ya shirya tsab don jagorancin jihar Katsina. Shiri irin na fitar da kitse daga wuta. 

Kundin da ya gabatar ya kunshi manufofi da kudure kuduren sa game jihar Katsina da kuma hanyoyin da za a cimma su. Wadannan kudurori ba shaka idan an aiwatar da su bakwai za su tabbatar da dorewar cigaban da aka samu karkashin jam'iyyar APC ba ne kawai har ma za su samar da sabuwar jihar Katsina. 

Manya daga cikin tanada tanaden su ne; harka tsaro, da fannoni ilmi, da harkar lafiya, da aikin gona, da samar da aikin yi, da zuba jari da masana'antu, da cugaban matsa, da inganta aikin gwamnati, da inganta birane da kuma raya karkara. 

Don samar da cikaken tsarin aiwatar da wadannan kudare kudare yanzu haka an nada wa su kwamitoci da su ka kunshi kwararu daga fannoni na rayuwa dabam dabam don zayyana hanyoyin da za a cimma wannan buri. 

Hausawa sun ce; gani ya kori ji. Wannan ne ya sa Dr. Radda ya shirya ya kuma aiwatar da rangadin kananan Hukumomin jihar Katsina guda talatin da hudu (34). A wannan tsarin an gudanar da rangadin da kusan shekaru arba'in ba a yi irin sa ba. Inda aka shiga kowace mabaza ta kansila watau ward guda 361. 

An gudanar da gangami ba tare da wata hatsaniya ko cin zarafi ko tashin hankalin wani ko wata al'umma ko jam'iyya ba. 

An shaida cewa baya ga zuga irin ta Buhari ba a samu wani gangami da ya samu goyon bayan talakawa kamar gangamin da Dr. Radda ya gudanar ba. 

Gangamin da aka gudanar da shi ba tare da sojojin haya ko hayaniyar 'yan banga ko 'yan daba ko ma su gurbatattun halaye ba. 

A lokacin rangadin, Dr. Radda da tawagar sa sun gane wa idanuwan su halin da kowane lungu da sako na jihar Katsina ke ciki. 

Sun kwana cikin garuruwan, sun ci sun sha irin abinci da jama'a kowace karkara ke ci da sha. Sun kuma ga cigaba da akasin haka na wadannan yankunan. 

Maganar tsaro wadda ita ce kan gaba, Dr. Radda ba sai an ba shi labari  ba, don shi ganau ne ba jiwau ba, don ta  shafe shi kai tsaye,  ya rasa danuwansa an kuma kama danginsa. 

Saboda haka ne ma tawagar sa ta ratsa duk wani lungu da ake jin  'yan ta'adda  sun yi katutu don nuna wa al'umma cewa ya na tare da su a duk halin da su ka tsinci kan su. Kuma in sha Allah ba zai Sarara ba  har sai ya tabbatar da sun samu waraka daga wannan anoba. 

Tunkarar harkar tsaro kamar yadda ya nuna, na bukatar jagoranci da kuma kawar da dalilan da ya jawo shi. Wadannan dalilan kuwa sun hada da cin hanci da rashawa da halin ko in kula ga rayuwar marasa galihu da rashin kula da muhali wanda shekaru sha shida (16) da PDP ta yi kan mulki su ka haddasa. 

Saboda haka ya yi tanadin yadda za a shawo kan wadannan illoli ta kawar da kuruciyar bera a harkar rayuwar mu ta yau da kulum da kuma fadada hanyoyin samar da aikin yi da sababbin dubaru na noma da kiwo. 

Irin wadannan kyawawan manufofi da kudurori na Dr. Radda ya jawo hankalin shugabanni, musamman na gargajiya da na addini inda su ka ayyana goyon bayan su a gare shi. 

Bisa gamsuwa da sahihancin Dr. Radda Kungiyoyin matasa, da mata, da na addinai, da kabilu, da na sana'oi da na ma'aikata da sauran su, sun nuna goyon bayansu a gare shi. Kai kamar yadda Hausawa kan ce; ko da na ka, ka so nagari, harma wadansu 'yan jam'iyyun sun bar tafiyar su zuwa ta Dr. Radda. 

Saboda haka yayin da mu ke tunkarar zaben Asabar mai zuwa, mu na fatan ma su jefa kuri'a a jihar Katsina za su kara maimata halarci da su ka yi a baya.

Ya kamata mu kara jinjina ma jama'a jihar Katsina musamman wadanda ke fama da farmakin  ta'addanci saboda bijire wa  makircin makiyan al'umma, ma su zubda jinin su da tagayyara su don goga kashin kaji ga jam'iyyar APC saboda kawai su samu damar da za su mulke su. 

Mu na fatan zaku kara hakuri da jajircewa  don kaucewa duk wani  tunzuri da za a yi don kawar da ku daga mikakkiya hanayar da ku ka taho. 

A karshe zan rufe da kalaman da Dr. Radda ya rufe jawabin sa yayin da aka yi mahawara tsakanin 'yan takara da BBCHAUSA ta shirya a jihar Katsina. In da ya ce:

"Amma kamar yadda ma su fada su ka fada mulkin nan dai Allah ke bada shi. Ba ka da wani wanda ke bada shi sai Allah. Amman abunda mu ka yi nan cikon shari'a ne, mu shiga jam'iyya, mu nemi mutane, mu nemi takara, amma bada mulki sai Allah ke badawa. Amma mutanen katsina an haska hitila... ya kamata mutane su yanke wa kansu hukunci kuma su sani cewa Allah zai tambaye su akan hukuncin da su ka yanke ko mai kyau ko maras kyau"

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post