Dikko Radda Ya Ce Zaɓen 2023 Ya Fi Kowane Zaɓe Da A Ka Yi A Nigeria Sahihanci

Dr. Dikko Umar Radda

Zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam'iyyar APC, Dr. Dikko Umar Radda, ya aiyana zaɓuɓɓukan da a ka yi a 2023 da zaɓuɓɓukan da su ka fi kowaɗanne a Nigeria.

Dr. Radda ya faɗi haka ne da ya ke jawabin godiya bayan ya karɓi takardar tabbatar ma shi da lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina na 2023. 


Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ce ta damƙa ma zaɓaɓɓen gwamnan takardar lashe wannan zaɓe a hedikwatar ofishinta na jihar Katsina. Sauran ƴan takara da su ka amshi irin wannan takarda sun haɗa da mataimakin gwamna mai jiran gado, Faruk Lawal Joɓe da ƴan majalisar dokokin jihar Katsina 31 daga cikin 34.


Dr. Radda ya gode ma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda a ƙarƙashin jagorancinshi ne a ka sami wannan gagarumar nasara. Ya kuma gode ma shugaban majalisar gangamin yaƙin zaɓe ta APC a jihar Katsina, Arc. Ahmed Musa Ɗangiwa, da hukumar zaɓe da kuma al'ummar jihar Katsina da du ka zaɓe shi.

An gudanar da bukin a farfajiyar hukumar zaɓen da ke Katsina, wanda Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya halarta, tare da shugabannin kungiyoyi, da na Addini da masarautun gargajiya.

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post