Daga Gwagware Media Reporters
Gidauniyar Gwagware Foundation, mallakin zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda, ta ƙaddamar da rabon kayan abinci na azumi ga marayu a dukkanin ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jihar Katsina.
Gidauniyar ta Gwagware Foundation ta kai aƙalla shekaru takwas ta na bada wannan tallafi domin samun ladar azumin watan Ramadan.
Da ya ke jawabi, Dr. Dikko Radda, ya bayyana cewa wannan tallafi tsawon shekaru takwas kenan ana gabatar da shi domin kawo sauki ga marayu da marasa galihu a cikin watan Ramadan. Ya cigaba da cewa cikin amincewar Allah, za ya ƙara linka wannan tallafi domin samun rabauta a ranar gobe ƙiyama. Daga karshe, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su haɗa kai domin ciyar da gajiyayyu da marayu a jihar Katsina.
Malam Muhammad Abu Ammar, ya bayyana wannan taro a matsayin taro da duk shekara ya ke halarta, wanda a cewar shi, irin wannan tallafi ne ya kai Gwagwaren Katsina a matakin nasara. Ya bayyana falalar taimakon gajiyayyu a addinin musulunci da kuma fatan Allah ya bada ladar aikin alkhairi.
Kayan abincin da aka raba sun haɗa da buhun shinkafa 170, buhun gero 170, sannan taliya katan 1000.
An gudanar da taron a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris 2023, wanda ya yi daidai da 1 ga watan Ramadan, hijira 1444, a babban ofishin godauniyar da ke hanyar Ɗanɗagoro, Katsina.
Tags
Hausa News