Gwamna Masari da Magoya bayan APC Sun Yi Zagayen Murnar Nasarar Tinubu

Daga Gwagware Media Reporters 

A ranar Laraba 1/03/20223, dubban ƴan jam'iyyar APC su ka fito kan tituna suna taya zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu murna.


Shi ma mataimakin dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC, Hon. Faruq Lawal Joɓe, ya na cikin jerin gwanon da su ka bi ta manyan tituna, daga bisani kuma su ka yi dandazo a dandalin jama’a (people's square) na gidan gwamnati.

Da ya ke jawabi ga magoya bayansa, Gwamna Aminu Bello Masari ya ce Katsina ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta mara wa APC baya kuma in Allah Ya yarda za mu samu nasara a zaɓe mai zuwa.

“Mun yi imanin cewa Katsina za ta ci gaba a karkashin Dikko Radda da kuma Naijeriya a ƙarƙashin Ahmed Bola Tinubu, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

“Mu godewa Allah da ya yi biyayya ga gwamnatin APC bisa la’akari da irin wahalhalun da mutane ke ciki musamman canjin kuɗaɗe, taɓarɓarewar naira da ƙarancin man fetur amma duk da haka, ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa da ya haɗa da ƴan takarar majalisar wakilai tara, da dukkan kujerun sanatoci 3 a jihar.

“A zaɓen watan Maris, Insha Allahu, duk ƴan takarar APC za su lashe kujerunsu ba tare da tangarɗa ba, domin Dikko ne kaɗai ɗan takara da mu ke da shi wanda zai iya tuƙin jihar.”

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post