Daga Katsina Gazette
Ƙasa da awanni 24 da ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Naijeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sauka birnin Katsina a ranar Laraba.
Sabon angon Naijeriyar, Bola Tinubu, ya sauka a jihar ta Katsina ne, bayan an ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Naijeriya a cikin daren ranar Talata, inda ya sauka a filin sauka da tashin jiragen saman jihar ta Katsina.
A yayin saukarsa, Tinubu, ya sami tarbar gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu.
Tinubu da tawagarsa sun shigo Katsina, daga bisani su ka wuce Daura don ganawa da shugaban ƙasa Buhari da ke hutun zaɓe yanzun haka a gidansa da ke Daura.
Tags
Hausa News