Daga Gwagware Media Reporters
A ranar Alhamis 9/3/2023, Tsohon ɗantakarar mataimakin gwamna na NNPP, Engr. Muttaƙa Rabe Darma, da tsohon ɗantakarar sanata na shiyyar Daura, da ɗumbin magoya bayan su su ka bayyana goyon bayan nasu ga ɗantakarar Gwamnan na APC.
Sun aiyana wannan ƙuduri ne a madadin sauran shugabannin Jam'iyyar da dubban magoya bayansu, a wani taro da su ka kira a Katsina tare da ɗantakarar Gwamna na jam'iyyar APC, Dr. Dikko Radda domin bayyana goyon bayansu gareshi a ɗakin taro na Munaj Event Centre, Katsina.
Da ya ke bayyana dalilinsu na yin wannan mubayi'a ga ɗantakarar Gwamnan na jam'iyyar APC, Injiniya Muttaƙa Rabe Darma, ya bayyana cewa su Jihar Katsina su ke kallo kuma sun aminta da Dikko Umaru Radda shi ya sa su ka yi wannan mubayi'a gare shi, domin samar da shugabanci da zai ciyar da Jihar gaba.
Muttaƙa Rabe Darma, ya sha alwashin ba shi kowace irin gudummawa da goyon baya domin ganin ya zama Gwamnan jihar Katsina. Kuma, kamar yadda ya faɗa, ita wannan Jam'iyya tana da tsarin shugabanci tun daga mazaɓar karamar hukuma, har zuwa Jiha kuma da izinin Allah da su da masu binsu sai sun tabbatar da nasarar Dr. Dikko Radda, kamar yadda ya ce.
Daga karshe kuma ya tabbatar cewa suna cikin Jam'iyyar NNPP kuma suna tare da ita amma suna goyon bayan ɗantakarar Gwamna na APC, Dr. Dikko Umaru Radda ne saboda cancantarsa da gogewarsa da kuma iliminsa.
Shi ma da ya ke gabatar da nasa jawabin, Dr. Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa "Abinda ya haɗa mu nan jihar Katsina da kuma tunanin ya za'a yi jihar Katsina ta ci gaba.
"Domin mu ƴan jam'iyyar APC ne ku kuma ƴan jam'iyyar NNPP ne, amma kuka zo domin mu haɗu mu yi abu guda domin mu ciyar da jihar Katsina gaba. Abinda muka sani munyi takara kuma mun ce Allah ya yi mana hukunci da abinda ke cikin zukatanmu.
"Hakan ne ya sa mu ka ce bari mu haɗu da ku domin mu kawo cigaban da muke da buƙatar mu kawo ma jihar Katsina domin an wuce lokacin da za'a yi yaudara.
"Kuma an wuce lokacin da za'a yi cinikin jihar Katsina, kuma ina tabbatar ma ku shugabannin da suka zo wurina babu wanda ya ce man yana son wani abu ko da masinja ne a wurina, bare mu rubuta takardar yarjejeniyar raba kujeru.
"Amma abinda suka ce man shi ne suna so in kula da amanar al'ummar jihar Katsina da adalci kuma in yi ma wannan jam'iyya ta NNPP adalci. Saboda haka ina tabbatar maku idan Allah ya bani wannan dama zan kasance mai adalci ga al'ummar jihar Katsina baki ɗaya."
Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa tare da Sani Liti Ƴankwani
Shi ma da yake gabatar da nasa jawabin, daraktan yaƙin neman zaɓen ɗantakarar Gwamnan na jam'iyyar APC, Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa, ya bayyana cewa, "Jam'iyyar NNPP, jam'iyya ce wadda ta ginu da mutanen APC domin kusan ƴaƴan jam'iyyar APC ne, su ka gina ta. Wanda wasu dalilai su ka sanya suka kwashe kayansu zuwa wannan jam'iyya ta NNPP. Saboda haka ina tabbatar maku wannan dawowa da akayi godiya ce ga Allah kuma ina tabbatar maku wannan jam'iyya ta APC za ta yi maku adalci kuma za ta yi tafiya da ku ta amana."
Ɗantakarar sanata, kuma jigo a jam'iyyar NNPP, na jihar Katsina, sanata Abdu Ƴandoma, na ɗaya daga cikin waɗanda su ka maganta a wurin taron, tare da bada cikakken goyon bayansu wajen nasarar Dr. Dikko Umar Radda a matsayin Gwamnan jihar katsina.
Taron ya samu halartar ɗantakarar mataimakin Gwamnan Jihar Katsina na Jam'iyyar APC, Faruq Lawal Joɓe, shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Katsina, Alhaji Sani Liti Ƴankwani, Alhaji Haruna Mato, Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa, Murtala Isah Ƙanƙara, Wamishinan Albarkatun Ruwa, Musa Adamu Funtua, da sauransu.
Tags
Politics