Zaɓen Radda: Jinjina Ta Musamman

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda

Daga Adamu S. Ladan

Asabar da ta gabata, sha takwas ga watan Maris, 2023, ƴan Najeriya sun sake kafa tarihi. 

Tarihin da ya kunyata  waɗanda ba sa wa ƙasar fatan alkhairi. Waɗanda su ka hakaito cewa ƙasar za ta shiga ruɗani lokacin gudanar da zaɓen gwamnono da ƴan majalisun jihohi bayan sun kasa cimma burin su a zaɓen da ya gabata. 

Zaɓen na gwamnoni da ƴan majalisun jihohi da aka aje za a gudanar da shi sati ɗaya kafin wannan lokaci, an ɗage shi zuwa ƙarshen satin da ya gabata saboda uzurin da hukumar zaɓe ta bayar na cika ƙa'idar doka. 

Wannan kuwa ya zama tilas don kada a ba wa waɗanda ke hasashen rashin nasara a zaɓen kafar kawo cikas ta amfani da shari'ah su dagula lissafi. 

 Zaɓen dai an gudanar da shi cikin lumana kamar yadda hukumar zaɓe ta shirya a jihohi 31 daga cikin 36 da ke faɗin kasar nan. 

Mutanen Najeriya sun ba maƙiyan ƙasar kunya inda su ka yi fitowar farin-ɗango don sauke nauyin su na ƴan ƙasa. Inda su ka zaɓa kuma a ka  ba su abin da su ke so. 

Kamar yadda su ka yi a zaɓen da ya gabata makonni uku da su ka wuce sun jefa ƙuri'un su sun bi doka sun yi abinda ya dace. 

Duk da haka a ɗaiɗaikun wurare wasu ɓata gari waɗanda ba su da ta ido da iyayen gidansu su ka ɗora su bisa mummunar tarbiya sun bijiro da baƙar al'adar nan da tuni an manta da ita ta yunƙurin satar akwati, ko amfani da makamai don razana ma su kaɗa kuri'a da kuma waɗansu hanyoyin karkatar da hankalin masu zaɓe daga zaɓin cancanta. Sai dai jami'an tsaro da sauran al'umma sun yi rawar gani wajen daƙile su da tabbatar da cewa masu waɗancan baƙaƙen aniyoyi ba su yi nasara ba. 

A jihar Katsina, masu jefa ƙuri'a sun ajiye bambamce-bambancen jam'iyya su ka zaɓi cancanta, inda su ka zaɓi Dr. Dikko Umar Radda da mataimakinsa, Faruk Lawal Joɓe bisa rinjayen  ƙuri'u 859,892, ninkin  mai biye ma sa na jam'iyyar PDP,  Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, wanda ya sami ƙuri'u 486,620.

A nan dole a gode wa masu zaɓe a jihar Katsina saboda nuna kishi da wayewa a lokacin zaɓen, inda su ka sa makomar jihar a gaba fiye da biyan buƙatun ɗaiɗaikun su. 

Jinjina ta musamman ga jama'a da ke yankunan da ke fama da farmakin  ta'addanci saboda bijirewa makircin maƙiyan al'umma, masu zubda jinin su da tagayyara su don goga kashin kaji ga jam'iyyar APC saboda kawai su sami damar da za su mulke su.

Waɗannan yankunan sun nuna haƙuri da jajircewa matuƙa inda su ka bijire wa duk wata  tunzurawa don kawar da su daga miƙaƙƙiyar hanyar da su ka taho ta zaɓar APC. 

Bugu da ƙari, yabo na musamman ga magoya bayan manyan  jam'iyyun adawa na PDP da NNPP da PRP da su ka bar tafiyarsu su ka zaɓi Dr. Radda. Hausawa dai kan ce; ko da na ka, ka so nagari.

Haka ma wajibi ne a yaba ma kwamitin yaƙin neman zaɓe na jam'iyyar APC a jihar Katsina ƙarƙashin shugabancin jarumi mai hazaƙa, Jarman Kankiya, Arch. Ahmad Musa Ɗangiwa, wanda ya nuna juriya da haƙuri da jajircewa da basira wajen gudanar da jagorancinsa. 

 Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna, Rt.Hon Aminu Bello Masari, wadda ta samar da kyakkyawan yanayin da aka gudanar da zaɓen cikin cikkaken tsaro  ba tare da la'akari da kowane irin bambanci ba, ita ma ta ciri tuta ƙwarai. 

Wannan kuma shi ne ginshiƙin  kammala zaɓen cikin lumana ba tare da wata hatsaniya da ta yi sanadiyar hasarar rai ko dukiya a kaf faɗin jihar ba. 

Ƙungiyoyin sa kai da na sa ido na cikin gida da na waje ma sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da aka samu a zaɓen. Ƙungiyoyin sa kai musamman ta fannonin tsaro sun bada gagarumar gudummuwa ta cike giɓin da ke akwai inda jami'an tsaro ba su isa ba. Na tabbatar da wannan a ƙaramar hukumata ta Ɗandume, wadda ke fama da matsanancin matsalar tsaro. 

Za a yaba wa ƙungiyoyin sa ido saboda saɓanin wasu lokuta ko wurare inda irin waɗannan ƙungiyoyin ke shirya rahotannin ƙarya don su kawo tunzuri ko ruɗani ko su baƙanta zaɓen. A wannan karon kuma a jihar Katsina ba a samu hakan ba a fili. 

Jami'an tsaro ma sun nuna ƙwarewa yayin gudanar da aikin su. Sun sa jarunta da bin ƙa'idodin aiki na ba sani ba sabo wajen daƙile duk wata barazana da ta nemi ta dagula Lissafin gudanar da zaɓen. 

Yanzu dai a fili ya ke mutanen jihar Katsina sun zaɓi gwamna da aka yi wa jam'iyyar sa ruwan kuri'u kusa da dubu ɗari tara (900,000) tare  da rinjayen ƴan majalisu ɗari bisa ɗari.

Wannan na nuni da cewa masu  jefa ƙuri'a sun tattara soyayyar da su ka nuna wa manyan ƴan takarar shugaban ƙasa guda biyu, watau Tinubu da Atiku a jihar Katsina sun miƙa wa Dr. Radda. 

Lallai wannan babban tagomashi ne a siyasa. Sai dai hakan na tattare da babban ƙalubale ga zaɓaɓɓen gwamna mai jiran gado, Dr. Radda. Ƙalubale na kyakkyawan fatan da mutane su ke da shi a kan sa na zai iya fitar masu kitse daga wuta. 

Duk da cewa Dr. Radda tun yaƙin neman zaɓen sa ya yi ma mutanen jihar Katsina alƙawarin gudanar da mulki bisa doran adalci, ya sake jaddada haka bayan hukumar zaɓe ta ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamna. 

Ba ma shakku bisa cancantar Dr. Radda wajen fuskantar wannan ƙalubale. 

Kamar  yadda  mu ka  shaida ma jama'a kafin zaɓen ranar Asabar. Ɗan shekaru 53,  Dr. Radda gogaggen ɗan siyasa ne, ƙwararre kan harkar zuba jari, tsohon malamin makaranta, da aikin banki, kuma gogaggen masanin tafiyar da mulki.

Yayin yaƙin neman zaɓe ya nuna kansa a matsayin jagora, lafiyayye, tsayayye, mai dogaro da kansa, mai ilmi kuma kwararre a  fannoni na rayuwar aikin gwamnati da kuma mai zaman kansa. 

Ya kuma nuna cewa shi ba yankan rake ba ne, ko ɗan bani na iya ba.  

Baya ga fitowa daga babban gida, Dr. Radda ya sami kyakkyawar shaida cewa mutum ne mai tarbiyya da halaye nagari da iya mu'amala da hangen nesa.

Ya na kuma da tausayin na ƙasa da marasa galihu. Ya kan nuna matuƙar damuwarsa kan al'amarin al'umma. 

Duk da waɗannan halaye, Dr. Radda ba mutumin da ake yi wa hawan ƙawara ba ne musamman kan abin da ya shafi gudanar da mulki da jama'a. Ya iya tawaye akan duk wata manufa da ya ke ganin ba za ta haifar ma jama'a ɗa mai ido ba. 

Waɗanda su ka yi aiki da shi ƙut-da-ƙut sun ba da shaida cewa ya na da tsinkaye da hangen nesa wajen ɗaukar shawara da yanke hukunci. Ya na da kuma gogewa da tsantsani wajen tusarrafi da dukiyar al'umma. 

Dr. Radda ya nuna cewa jagora ne nagari. Daga tanade-tanaden da ya yi cikin kundin da ya gabatar wa jama'a zuwa rangadin da ya gudanar da kalaman sa ya nuna cewa ya shirya tsaf don jagorancin jihar Katsina. Shiri irin na fitar da kitse daga wuta. 

Kundin da ya gabatar ya ƙunshi manufofi da ƙudure-ƙuduren sa game da jihar Katsina da kuma hanyoyin da za a cimma su. Waɗannan ƙudurori ba shakka idan an aiwatar da su ba kawai za su tabbatar da ɗorewar cigaban da aka samu ƙarƙashin jam'iyyar APC ba ne har ma za su samar da sabuwar jihar Katsina.

Manya daga cikin tanade-tanaden su ne; harkar tsaro, da fannonin ilmi, da harkar lafiya, da aikin gona, da samar da aikin yi, da zuba jari da masana'antu, da cigaban matasa, da inganta aikin gwamnati, da inganta birane da kuma raya karkara. 

Don samar da cikakken tsarin aiwatar da waɗannan ƙudure-ƙudure yanzu haka an naɗa wasu kwamitoci da su ka ƙunshi ƙwararru daga fannoni na rayuwa daban-daban don zayyana hanyoyin da za a cimma wannan buri. Mu na sa ran ba da daɗewa ba za a ƙaddamar da waɗannan kwamitoci don fara aikin su.

Hausawa sun ce; gani ya kori ji. Tuni dai Dr. Radda ya gudanar da rangadin kananan Hukumomin jihar Katsina guda talatin da hudu (34). A wannan tsarin an gudanar da rangadin da kusan shekaru arba'in ba a yi irin sa ba. Inda aka shiga kowace mazaɓa ta kansila watau ward guda 361.

A lokacin rangadin, Dr. Radda da tawagarsa sun gane wa idanuwansu halin da kowane lungu da saƙo na jihar Katsina ke ciki.

Sun kwana cikin garuruwan, sun ci abinci kuma sun sha irin ruwan da jama'ar kowace karkara ke ci da sha. Sun kuma ga cigaba da akasin haka na waɗannan yankunan. 

Saboda haka ana sa ran gwamnatin da za a kaddamar ba za ta ɗauki dogon lokaci ba wajen tunkarar abin da ke gaban ta. 

Fata ita ce, Allah Ya kama hannun sa Ya yi ma shi jagora wajen zaɓo wazirai na gari da za su tallafa ma sa aiwatar da wannan gagarimin aiki. 

Ya na da kyau kuma mu yi amfani da ibada da mu ke a wannan wata mai alfarma don yi wa Allah godiya da Ya sa aka yi zaɓen lafiya sannan Ya zaɓa mana mafi alkhair. Haka kuma mu nema ma sabon gwamna jagorancin Ubangiji da kariya wajen gudanar  da mulkin jihar Katsina. 

 Yayin da mu ke wa sabon zaɓaɓɓen gwamna fatan alkhair ya na da kyau kuma jama'a su yi amfani da wannan lokaci da ake shirye-shiryen miƙa mulki wajen bayar da nagartattun shawarwari da za su taimaka don ciyar da jihar Katsina gaba. 

Ga waɗanda Allah bai ba su nasara ba, su ma mun jinjina ma su da su ka shiga zaben. Shigar su ta haska kuma ta ba jama'a dama su ka zaɓi mafi nagarta. Ta kuma zaburar da jam'iyyar mu ta hanyar abinda a ke cewa in kana da kyau ka ƙara da wanka.

Saboda haka ya na da kyau a wannan gaɓar a bada shawara ga waɗanda ba su sami nasara ba da su rungumi ƙaddara kamar yadda su ka sha faɗa lokacin yaƙin neman zaɓensu. Maimakon ɗaukar matakan da ba za su haifar da ɗa mai ido ba, ya kamata su bada haɗin kai ga wanda Allah Ya zaɓa ta hanyar yin adawa mai ma'ana da a ko da yaushe za ta saita gwamnatin da za a kafa bisa tafarki ma daidaici. 

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post