Zan Fara Aiki Tuƙuru Daga Ranar Da Aka Rantsar Da Ni – Inji Dikko Raɗɗa


Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa

Zan fara Aiki tuƙuru daga ranar da aka rantsar da ni – Inji Dikko Raɗɗa

Zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Katsina, yace ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyuka ga al'ummar jihar Katsina idan aka rantsar da shi.

Dr. Dikko Raɗɗa, wanda aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris.

Katsina Post ta tattaro cewa, ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da yake ƙaddamar da kwamitocin nazarin yadda zai gudanar manufofinsa a ranar Laraba.

Zaɓaɓɓen Gwamna, Dr. Dikko Raɗɗa tare da Farfesa Ahmed Mohammed Bakori

Ya bayyana cewa, dalilin da yasa aka kafa kwamitoci a yanzu shi ne, su yi duk mai yiwuwa don ganin an samar da takardar manufofin su kafin ranar 29 ga Mayu, ta yadda ba za mu ɓata lokaci ba wajen taka rawa wajen tafiyar da al’amuran jihar Katsina.

Yace ya ƙirƙiro tsare-tsarensa a matsayin wani ɓangare na abin da yake son yi wa jihar Katsina idan ya zama Gwamnan jihar.

Ya ƙara da cewa, sun gayyato masana a ɓangarori daban-daban na wannan takarda da su sake duba ta tare da gabatar da bayanansu da nufin tace ta ta zama sahihiyar takarda. Yace wajibi ne na kwamitocin su tsara dabarun aiwatar da ƙudirinsa.

Kazalika, ya buƙaci kwamitocin da su jajirce wajen ganin an samu nasara cikin lokacin da aka ba su. Yace akwai sassa 11 a cikin takardar da suka haɗa da; Sake Fasalin Ayyukan Gwamnati, Tsaro, Aikin Gona, Ilimi da kuma Gyara Fannin Lafiya, Kula da Jama'a, Sake Fasalin Ƙasa, Cibiyoyin Gargajiya da Kwamitocin Harkokin Addini.

Ya kuma yi alƙawarin cewa, kwamitocin za su yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun aiwatar da aikin cikin wa’adin.


Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post