Dandalin WhatsApp Ya Saya Wa Mabuƙata Kayan Abinci Na Milyoyin Naira A Katsina


Daga DCL Hausa 

Wata gidauniya da ke karkashin wani Dandalin WhatsApp mai suna KATSINA CITY NEWS, sun tattara kudade har Naira miliyan biyar da dubu dari daya da sha bakwai, inda suka rika taimakon mabukata a lokacin Azumin watan Ramadan.

Dandalin na WhatsApp wanda na 'yan Jihar Katsina da suka fito daga mabambantan jam'iyyun siyasa da ra'ayoyi daban-daban, sun hadu karkashin inuwa daya domin ci gaban Jihar Katsina. 

Kwamitin na Azumi, wanda Dandalin ya kafa yana karkashin shugabancin Alhaji Lawal Aliyu Daura mni, tsohon Shugaban Ma'aikata na Jihar Katsina, yana da membobi kamar haka:- Hajiya Mariya Abdullahi Bakori, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina, Alhaji Lawal Rufa'i Safana, Alhaji Dauda Kurfi, Hajiya Murja Saulawa, Barista Ahmad Danbaba Batsari. Alhaji Muntari Lawal Kofar Soro, Alhaji Hamza Yunusa Jibia, SSA Sabo Musa Hassan da sauran su.

Wannan ita ce shekara ta hudu da wannan kwamitin ke aikin sa duk lokacin Azumin watan Ramadan.

A bana 2023, kwamitin ya bai wa gidajen mabukata 500 abinci da kudin cefane. Kowane gida ya samu shinkafa, garin masara, taliya, magi da man girki da kuma dan kudin cefane.

Kwamitin ya sako matasa bakwai daga gidan yari bayan ya biya masu 'yan kananan tara, ya kuma biya wa mata 20 kananan tara na bashi da aka kai su kotu a kai.

Kwamitin ya kuma rika kai abinci dafaffe a gidan baki da asibiti domin marasa lafiya da akan kawo daga karkara ba su da kowa a cikin Katsina.

Kudaden da ake wannan aikin, 'yan Dandalin da ke WhatsApp mai suna KATSINA CITY NEWS ne ke tattarawa a tsakaninsu. Mai Naira dubu daya, wani dubu 100, har sama da haka. Da haka ake tattara kudin ana wannan aikin da su.

Muhammad Danjuma shi ne mawallafin jaridun yanar gizo na KATSINA CITY NEWS da mujjalar KATSINA CITY NEWS, Shi ne wanda ya kirkiri dandalin a shekarar 2015, kuma ya tattara mutane daban-daban 'yan Katsina domin musayar labarai da tattauna abin da ya shafi Jihar Katsina da kasa baki daya.

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post