Daga: Surajo Ƴandaki,
Edita, Mobile Media Crew.
A zaman majalisar na ranar Laraba 05/4/2023, ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar Rt. Hon. Tasi'u Musa Maigari Zango, majalisar ta tantance membobin hukumar guda biyu.
Membobin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Katsina da majalisar ta tantance sun haɗa da: Alhaji Adamu Salisu Ladan, daga ƙaramar hukumar Ɗandume; Hon. Bala Sani Muhammad Yaya, daga ƙaramar hukumar Ingawa; Alhaji Ahmed M. Bindawa, daga ƙaramar hukumar Bindawa; Alhaji Dauda Muhammad Kurfi, daga karamar hukumar Kurfi.
Adamu Salisu Ladan, Kwamishinan Dindindin na Hukumar Zaɓen Jihar Katsina
Sai Membobin sabuwar hukumar kula da ayyukan majalisar dokoki da majalisar ta tantance sun hada da: Rt. Hon. Sani Sa'idu Fago, daga ƙaramar hukumar Sandamu; Alh. Abubakar (Maidanja) Ibrahim Malumfashi, daga ƙaramar hukumar Malumfashi; Mustapha Ibrahim Zango, daga ƙaramar hukumar Zango.
Duk a zaman majalisar na ranar Laraba an aje tare da karanta rahoton binciken kwamiti na musamman a kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a watan huɗu na shekara ta 2022, wanda memba a kwamitin, Hon. Lawal H. Yaro ya karanta ya kuma aje rahoton binciken a gaban zauren majalisar. Rahoton binciken ya tabbatar da ƙin amincewar majalisar.
An ƙara tantancesu a naɗa su membobin hukumar da Gwamnan ya buƙata kwanakin baya. Hakazalika, binciken ya yi gaba da shugaban hukumar zaɓen ta Jihar daga kan mukaminsa.
Daga ƙarshen zaman majalisar na ranar Laraba, an baiyana jaddawalin gudanar da kare kasafin kuɗin ƙananan hukumomin Jihar Katsina 34, wanda shugaban kwamitin kula da ƙananan hukumomi da masarautu na majalisar, Hon. Garba Husaini Dankanjiba, ya baiyana.
Tags
Hausa News