Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Faruk Lawal Joɓe
Daga Isah Miqdad, SSA Digital Media to Katsina State Governor
Gwamnatin jihar Katsina ta fara wani shiri na musamman don daukar matasa 2,400 domin magance matsalolin tsaro dake addabar wasu sassan jihar.
Bayan dauka da ba matasan horo, za su hadu da jami'an tsaro domin kara samar da tsaro a kananan hukumomi 8 da suka sha fama da matsalolin tsaro a jihar.
A ranar Juma'ar nan 7th Juli, 2023 ne dai mataimakin Gwamnan jihar Hon Faruq Lawal Jobe ya kaddamar da rarraba takardun cikewa na 'form' ga shugabannin kananan hukumomin da lamarin ya shafa. Daga nan, shugabannin kananan hukumomin za su zakulo tare da tantance matasan, su rarraba musu wadannan takardun cikewa domin zuwa mataki na gaba na kokarin kare rayuka da dukiyoyin al'ummominsu.
Gwamnatin jihar dai ta ce babban makasudin wannan yunkuri, shi ne don karin maganar nan ta Hausawa dake cewa "da dan gari, a kan ci gari". Wadannan matasa sun san lungu da sako na yankunansu, don haka za su tallafi jami'an tsaro wajen bi kokuwa-kokuwa don fatattakar masu aikata assha a cikin al'umma.
Idan dai zaku iya tunawa, lokacin yakin neman zabe, Malam Dikko Umaru Radda ya yi alkawarin cewa tsaro na a sahun gaba a cikin alkawurran da ya daukar wa al'ummar jihar, inda ya buga misali da zuwa har wuraren da ake ganin ba su shiguwa ta dalilin ayyukan 'yan bindiga a lokacin yakin neman zabe.
A lokacin rarraba wadannan takardun cikewa na 'form', mataimakin Gwamnan jihar Katsina Hon Faruq Lawal Jobe ya ce, "sanin kowane cewa Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya sha alwashin kawo karshen ayyukan ta'addanci musamman ma a kananan hukumomin da lamarin ya yi kamari, da sauran sassan jihar".
Mataimakin Gwamnan ya ce an shirya daukar wadannan matasa, su hadu da jami'an tsaro su ba su horo na musamman domin su tallafi jami'an tsaron wajen samar da tsaro.
Hon Faruq Lawal Jobe ya ce za a dauki matasa 300 a kowanne kananan hukumomin 8 da lamarin ya fi kamari. Sannan ya ce za a dauki matasan da ba su wuce shekaru 35 da haihuwa ba kuma masu tarihin ladabi da biyayya a cikin al'umma.
Ya bukaci jagororin kananan hukumomin da su saka tsoron Allah wajen zaben mutane nagari kuma masu kishin dake son tsare rayuka da dukiyoyin al'ummominsu don a cimma nasara.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Arch. Ahmad Musa Dangiwa ya ce kwanaki kalilan da suka shude, gwamnatin jihar ta gana da shugabannin kananan hukumomi, inda aka tattauna sosai game da batun samar da karin matasan da za a yi wa lakabi da "Matasa masu samar da tsaro a yankunansu". Ya ce yin hakan zai taimaka sosai wajen samar da tsaro a yankunan.
Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Ahmad Musa Ɗangiwa
Ahmad Musa Dangiwa ya yi bayani dalla-dalla na hanyoyin da za a bi wajen daukar matasan aikin samar da tsaro. Ya kuma yi kira ga jagororin kananan hukumomin da su zabo nagartattun matasa tare da tsarin da za su bi, don gudun guje wa kitso da kwarkwata.
Tags
Hausa News