By Lawal Rufa'i Safana
Watau ina ganin ba daga horas da yaran nan zuwa tura su wurin aiki aikinsu ya tsaya ba. Gaskiyar Allah farawa ce kawai wannan, domin akwai abubuwan da za su sa suyi aikin yadda ya dace.
Ina so a fahimci cewar yaran nan fa an horas da su ne a matsayin masu kare al'umma. To, abin dubawa shine bamu da tsararrun al'ummomin da zasu ba waɗannan dakarun ƙwarin gwuiwa na gudanar da aikinsu. Idan an ɗauke su an aje a ƙaramar hukuma aka haɗa su da ƴan sanda akayi shiru ko aka haɗa su da chairman akayi shiru duka wannan bai nuna cewa su masu kare al'umma bane saboda ba ma zasu iya shiga cikin ƙauyukan ba cikin kwanciyar hankali balle aikin ya yiwu ba tare da goyon bayan al'ummar da suke karewa ba.
Babban mataki da ya kamata ya biyo bayan tura su shine ayi shiri a gudanar da majalisi na tattaunawa da al'umma da shuwagabannin al'umma na kowane garin Magaji domin a tattauna da manyan gari a tabbattar da kyakyawar fahimta da alaƙa tsakanin sabbin dakarun nan da masu faɗa a ji na ƙauyukan mu da garuruwan mu. Shi wannan dandali ya kamar zama majalisi ne na shuwagabannin al'ummar kowa ne ƙauye kuma a tabbatar majalisin ya kunshi shuwagabannin fulani da manoma da dagatai da limamai dasu sarkin kasuwa, sarkin fawa da na matasan garin da sauran irin waɗannan shuwagabanni. A nuna masu dalilin ƙirƙiro wannan dakaru na da irin zamantakewa da alaƙar da ake bukata tsakanin su da al'umma, a nuna wa shuwagabannin fulani dake cikin majalisin cewar zaman kowa lafiya shine ayi tare ta arziki da lumana saboda idan ba haka ba to duka babu sauran wanda zaya zauna lafiya saboda yanzu dai ga wuta ga masara.
Shuwagabannin al'umma su tattauna hanyoyi da sharuɗɗa na alaƙa da zamantakewa tsakanin junansu da jinsin su da sana'oin su domin kowace al'umma ita ta san hanyar zaman lafiyar ta. Wannan tattaunawar za ta maido ƴan ta'adda da masu basu bayanai da yawa cikin hankalinsu saboda babbar hanya ta zaman lafiya da ci gaban ƙauyukan mu yanzu ya ta'allaƙa ne akan sa ido da sa baki da aikatawa na shuwagabannin dake zaune cikin al'ummarsu ko da yaushe, ba ɗan sanda ko soja ko ɗan siyasar da zai je ya leƙo ya dawo ba. Alaƙa ake bukata da tattaunawa da hukuntawa ta din din din a cikin kowace al'umma domin duk abinda ya bijiro nan take a'lumma ta ɗauki mataki kai tsaye tunda gashi yau Allah ya hore mata makami da dakaru na gwamnati ga hannu. Abinda ake bukata kawai shine haɗin kan dattawan gari da ƙauye har da shuwagabannin fulani dake wurin.
Al'amari ne wanda yake bukatar cikakken nazari da aiwatarwa da ya kamata gwamnati ta fuskanta don ya zama mataki na gaba don cin nasarar wannan kyakkyawan tsari. Idan ba ayi wani abu irin wannan ba aikin yaran nan cikin ƙauyukan dake bukatar aikin zai wahala ƙwarai da gaske. Ayi gaugawar shigo da al'ummomin da shuwagabannin kauyukanmu cikin tsarin nan a aikace ba a shawarce ba don yi ma yaran na kyakkyawan shimfiɗa ta cin nasara.
Allah yasa mu dace. Allah yayi jagora, amin.
Lawal Rufa'i Safana, tsohon babban sakatare ne a gwamnatin Jihar Katsina.
Tags
Articles