Hajiya Indo Umar Radda
Daga Ibrahim Nasir
Sama da marayu (500) da ƴaƴan marasa galihu ne suka amfana da tallafin kayan makaranta da littattafan rubutu a garin Radda daga yayar gwamnan jihar Katsina, Hajiya Indo Umar Radda.
A ranar Talata 31-10-2023 ne yayar gwamnan, Hajiya Indo Umar Radda, ta ziyarci makarantar Radda Model Primary School da makarantar Barebare Primary School, dukkansu dake cikin garin Radda domin bayar da wannan tallafi.
Da take gabatar da jawabinta Hajiya Indo Umar Radda ta bayyana cewa ta yi wannan tunani ne na bayar da wannan tallafi na kayan makaranta da littattafan karatu ga marayu da ƴaƴan marasa karfi domin su sami sauƙi.
A matsayinta na wadda ke aiki a ɓangaren inganta ilmi na hukumar ilmin bai ɗaya, watau SUBEB, Hajiya Indo ta ce ta san ciwon ilimi da buƙatar yin haka saboda yadda su ke shiga lungu da saƙo wajen aiki su na ganema idanunsu.
Shine tayi wannan ƙoƙarin domin ƙara ƙarfafa masu akan karatun su. Ta ce kuma ta yi la'akari da yadda gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ke da kyakkywan shiri a kan inganta harkar ilimi.
Daga karshe ta ce ta saudakar da wannan abu ga mahaifinsu, marigayi Maigarin Radda, Alhaji Umaru Barebarin Radda.
Shi ma a nashi jawabin, daraktan harkokin ilimi na shiyyar Katsina, Malam Mustapha Aliyu Kofar Sauri, ya yaba ma Hajiya Indo Umar Radda bisa wannan ƙoƙari. Ya kuma yaba da yadda ya iske aikin koyarwa a makarantun.
A nashi jawabin, sakataren ilimi na karamar hukumar Charanchi, Alhaji Abdullahi Dan'asibi, ya yaba ma Hajiya Indo bisa wannan ƙoƙari, inda ba ta manta da gida ba, ta zo domin al'ummarta. Ya ce su na ma ta fatan alakhairi da wannan ƙoƙari.
Abubakar Sani Larab na ɗaya daga cikin wanda suka tofa albarkacin bakinsu a wurin taron tare da yaba ma Hajiya Indo Radda, wadda su ke aiki a wuri ɗaya, kuma ta hango wannan hanya ta taimaka ma marayu da ƴaƴan marasa karfi.
Bayan kammala ƙadammar da kayan makarantar da littattafan, ta shiga azuzuwa domin ganin yadda yara ke ɗaukar karatu a matsayinta na malamar makaranta wadda ke da ƙwarewa a fannin.
Taron ya samu halartar ma'aikatan hukumar ilmi ta Charanchi da dai sauransu.
An samo labarin daga Mobile Media Crew
Tags
Hausa News